Tawagar ta ce akwai bukatar sauran mabiya addinai su fahimci menene musulunci domin zama tare.
Manyam manyan malaman addinin musuluncin sun fito ne daga babbar jami'ar nan ta Al'azahar to ziyarci garin Kaduna ne da zummar jawo hankalin al'ummar musulmi da kirista domin a zauna tare lafiya.
Shaikh Ahmad Muhammad Abubakar dan Najeriya dake cikin tawagar shi ya fasara jawabin da aka yi da Larabci zuwa Hausa. Yace dilin zuwa kasar shi ne wayarwa al'ummar musulumi kai akan menene sakon addinin musulunci. Yace musulunci addini ne na aminci, da kaunar juna, da kyautatawa juna. Yace su fahimci cewa idan wani musulmi ya yi masu abun da ba daidai ba shi aibin ke komawa gareshi ba musulunci ba. Idan aka gane za'a samu zaman lafiya.
Babban sakataren kungiyar Jama'atul Nasril Islam Dr.Khalid Aliyu ya yi karin haske game da abun da taron ke son cimma a karshe. Tawagar ta zo ne ta karfafa dawainiyar da musulmi ke yi wajen wanzar da zaman lafiya a kasar da ta yi fama da rikicin addini. Ana son a samu kyakyawan makwaftaka tsakanin musulmi da wanda ba musulmi ba. Tsakanin musulmi da musulmi kuma su zama masu tausayin juna da kaunar juna da taimakon juna da kuma yafewa juna.
Wasu mahalarta taron sun bayyana ra'ayoyinsu akan taron da ya hada da mabiya addinin kirista.
Yohanna Boro ma'akacin wata mijami'a ta kirista yace yana cike da farin ciki saboda abubuwan da ya ji a taron. Ya samu karfin gwuiwa cewa akwai begen samun zaman lafiya a kasar, musamman tsakanin kiristoci da musulmai.
Muhammad Suleiman yace an samu alheri a taron idan kuma an bi abun da aka fada a taron za'a samu fahimta tsakanin musulmi da kirista.
Sarah Dogo tace a zamanin nan irin taron da ake bukata ke nan domin ya hada kawunan musulmi da kirista da ma wanda bashi da addini domin a samu zaman lafiya.
Liman Awal Adam yace akwai kalubale cikin malaman dake koyas da addinin musulunci. Tarbiyantar da mutane a cikin sha'anin Manzon Allah (SAW) shi ne kawai mafita.
Ga karin bayani.