Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Bikin Ranar Dimokuradiyya Ta June 12 A Fadin Kasar


Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu

Ranar dimokuradiyya ba wai ta murnar nasarorin da Najeriya ta samu kadai ba ce; rana ce kuma ta girmama juriya da jajircewar al'ummar Najeriya.

Kamar kowace shekara, tun bayan da gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ayyana ranar June 12 a matsayin ranar Dimokuradiyya a duk fadin kasar a shekara ta 2018, wannan shekarar ma ranar 12 ga watan Yuni rana ce ta tuna wannan al'amari.

A wannan shekara ta 2023, a yau ne Najeriya ta ke gudanar da bikin zagayowar ranar dimokuradiyya kamar kowace shekara, tare da jinjina wa irin gagarumin cigaban da aka samu a tafiyar dimokuradiyyar kasar tare da yin la'akari da irin gwagwarmayar tarihin da ke ciki kafin samun wannan nasara.

Ranar dimokuradiyya ta dauki matsayi na musamman a tarihin Najeriya, domin murnar zagayowar ranar zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

Zaben wanda jama'a ke kallonsa a matsayin mafi sahihin zabe a duk tarihin kasar, Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola, ya wakilci jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) inda ya sami nasarar wanda ake zaton ya lashe zaben a wancan lokaci.

Zaben dai ya samu goyon bayan da ba a taba ganin irinsa ba a fadin kasar ba tare da nuna kabilanci, addini, ko yanki ba, lamarin da ke nuna nasarar dimokradiyya a tsakanin 'yan Najeriya.

Sai dai gwamnatin mulkin soja a wancan lokacin, karkashin jagorancin Janar Ibrahim Babangida, ta soke sakamakon zaben, lamarin da ya jefa al’ummar kasar cikin wani yanayi na rashin gamsuwa da kuma haifar da zanga-zanga.

Soke zaben dai ya gamu da fushin jama'a, yayin da 'yan Najeriya suka bayyana rashin gamsuwarsu da kuma neman a bi musu hakkinsu na dimokradiyya.

A shekarar 2018, gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokuradiyya a hukumance, wannan mataki na nuna irin nufin amincewa da sadaukarwar da aka yi a lokacin fafutukar tabbatar da dimokuradiyya da kuma girmama Cif MKO Abiola.

Tun daga wannan lokacin ne Najeriya ke bikin ranar dimokuradiyya a wannan rana domin tunawa da irin jajircewar da al'ummar kasar ke yi wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya.

Yayin da Najeriya ke ci gaba da samun nasara a tafiyar dimokuradiyya, kasar har ila yau na fuskantar kalubale na ci gaba, samun ilimi mai inganci, yaki da talauci da rashin daidaito tsakanin al’umma tare da samar da hadin kan al'umma su ne muhimman batutuwan da aka fi lura da tattauna a lokutan bukukuwan ranar Dimokuradiyya a kasar.

Yayin da Najeriya ke bikin ranar dimokuradiyya a wannan shekara 2023, al'ummar kasar na sabunta kudurinsu na tabbatar da akidun dimokuradiyya. Y zama abin tunatarwa cewa dimokuradiyya wani tsari ne da ake reno a ko wani lokaci da ke bukatar kokarin hadin kan 'yan kasa, shugabannin siyasa, kungiyoyin farar hula, da sauran masu ruwa da tsaki don karfafa cibiyoyin dimokuradiyya.

Ranar dimokuradiyya ba wai ta murnar nasarorin da Najeriya ta samu kadai ba, har ma tana girmama juriya da jajircewar al'ummarta.

Hakan ya kara tabbatar da cewa makomar Najeriya tana da haske, ta hanyar yin la'akari da ci gaban da aka samu da kuma kalubalen da ke gaban kasar, har yanzu Najeriya na ci gaba da share fagen samun nasarar dindindin a dimokuradiyya.

Yusuf Aminu

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG