Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranar 29 Ga Mayu, 2023, A Matsayin Ranar Hutu


Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023 a matsayin ranar da babu aiki ga daukacin ma'aikatan kasar.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023 a matsayin ranar da babu aiki ga daukacin ma'aikatan kasar.

A Ci Gaba Da shirye-shiryen mika Mulki da rantsar da zababben shugaban kasar Najeriya  na 16 Bola Ahmed Tinubu, gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023 a matsayin ranar da babu aiki ga daukacin ma'aikatan kasar.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a madadin gwamnati.

Babban sakatare a ma’aikatar harkokin cikin gida, Shuaib Belgore, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a. Ministan ya bayyana farin cikinsa ga daukacin ‘yan Najeriya kan wannan gagarumin biki tare da yaba musu bisa yadda suka yi imani da tsarin dimokuradiyya, kamar yadda zaben da aka gudanar a fadin kasar ya nuna wanda ya kai ga zuwan ranar rantsar da zababben shugaban kasa da mataimakinsa.

Minista Aregbesola ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da ba da goyon baya da inganta dimokuradiyya ta hanyar bin doka da oda da kuma kiyaye cibiyoyin dimokuradiyya. Ya kuma jaddada cewa dimokuradiyya wani tsari ne mai gudana, wanda ke bukatar bin ka’idojinta kamar bin doka da oda.

Bugu da kari, Ministan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su samar da akidar zaman lafiya da kaunar makwabtansu, yana mai jaddada cewa yanayin zaman lafiya na da matukar muhimmanci wajen aiwatarwa da cin moriyar dimokradiyya. Ya kuma yabawa ‘yan Najeriya bisa namijin kokarin da suke yi na ganin an ci gaba da gudanar da mulkin farar hula ba tare da katsewa ba da kuma samun nasarar mika mulki daga 1999.

Ministan ya kuma yi kira ga 'yan kasar da su guji duk wani nau'i na tashin hankali da sauran ayyukan da babu alheri a cikinsu kuma bazai kawo wa kasar da mai ido ba. Ya kuma ba su tabbacin cewa, ta hanyar yin aiki tare, za a yi amfani da karfin da al’umma ke da shi, wanda zai kai ga samun daukaka ta kowane fanni na ci gaban bil’adama.

Idan aka tuna a baya-bayan nan, Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya tabbatar da muhimmancin ranar 29 ga watan Mayu domin kaddamar da wannan aiki. Ya kuma yi gargadi game da masu barazana ga taron, ya kuma sha alwashin kare dimokuradiyyar Najeriya, yana mai jaddada cewa hukumar leken asiri ta kasa na sanya ido kan ayyukan wasu mutane da ke yunkurin kawo cikas ga tsaron kasa.

Yayin da al'ummar kasar ke dakon rantsar da sabon shugaban kasar, an karfafa wa 'yan Najeriya gwiwa da su rungumi zaman lafiya, da kiyaye martabar dimokuradiyya, da kuma bayar da gudunmawa mai kyau ga ci gaban kasa.

XS
SM
MD
LG