Hakan yana faruwa ne saboda hauhawar ma'aunin zafi kamar yadda masana sauyin yanayi su ka yi hasashe.
Jihohin arewacin Najeriya musamman wadanda suka yi iyaka da jamhuriyar Nijar wadanda ke fuskantar barazanar gurgusowar hamada suna fuskantar matsanancin yanayin zafi.
Masana sauyin yanayi a wani taro da suka gudanar a watan Fabrairun wannan shekara a Abuja sun yi hasashen cewa wasu jihohin Najeriya zasu tsintsi kansu cikin yanayin zafi fiye da kima.
Wannan yanayin ne ya sa yanzu jama'a ke fuskantar matsanancin zafi kuma ga azumi, abin da ya sa wasu suka zabi daukar wasu matakai na saukakawa rayukan su, kamar wasu da wakilin Sashen Hausa ya tarar dasu cikin wata fadama a Sakkwato sun fake cikin sanyi.
Batun daya ne har a jihar Kebbi kamar yadda wasu mazaunan jihar suka tabbatar.
Wannan yanayi a cewar masana sauyin yanayi yana faruwa ne sanadiyar wasu abubuwa da ake aikatawa musamman wadanda ke kawo dumamar yanayi da duniya baki daya ke fuskanta, tare da fafatukar ilimantar da jama'a akan illolinsa.
Ga rahoton da Muhammad Nasir ya aiko mana daga Sokoto: