Samar da tsaro da bukatar hukumomi su yi duk mai yiwuwa wajen maida wadanda suka guje daga mahallansu dalilin rashin tsaro, don samar da abinci a kasar, da wasu muhimman batutuwa ne suka mamaye karshen taron shugabanni da wakilan shiyya-shiyya na Majami’ar ECWA ta kasa da kasa a taronta na bana.
Shugaban ECWA Rabaran Stephen Panya-Baba ya ce sun yaba da kokarin jami’an tsaro amma dole gwamnati ta dauki matakan hukunta wadanda aka kama da ayyukan ta’addanci.
Shugaban ya kuma ce sun tattauna batun sasantawa tsakanin gwamnati da malaman jami’o’i don dalibai su ci gaba da karatu a kuma samar wa matasa ayyukan yi.
Rabaran Mathew Shado daga yankin Shiroro a jahar Neja, wanda shi ma ya halarci taron, ya ce al’ummarsu sun gudu daga mahallansu don haka suke neman agaji.
Shi ma Rabaran Dauda Nyam daga jahar Bauchi ya shawarci gwamanati da ta dauki kwararan matakan kawo karshen rashin tsaro a kasar.
Al’ummar Najriya dai na fatan ganin hukumomi za su inganta sha’anin tsaro ya yin da shugabanan addinai ke kara fadakarwar zaman lafiya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: