A rahoton da kungiyar CLEEN Foundation ta fitar ya zargi hukumomi kamar su EFCC da 'Yansanda da na Shige da ficin Najeriya wato Immigration da Kwastan da ICPC da dai sauransu. Akwai ma wasu hukumomin gwamnati da ma'aikatun gwamnati da rahoton ya ambata. Kungiyar ta ce 'yan Najeriya sun bayar da bayanai daban daban kan kowanensu kan matsalar cin hanci da rashawa.
'Yan Najeriya inji kungiyar sun ambaci hukumar EFCC musamman da matsalar cin hanci da rashawa. To sai dai ita hukumar ta EFCC ta yi watsi da rahoton tana cewa ana neman a shafa mata kashin kaji ne kawai domin a bata mata suna.Rahoton yana nuna EFCC tana gaba gaba sai 'yansanda da hukumar shige da fice ta immigration da ICPC da hukumar NEPA da kuma kwastan.
Kungiyar da ta yi binciken ta ce ta dauki duk matakan da suka kamata su tabbatar babu zargi ko kazap a cikin rahotonsu kamar yadda daya daga cikin shugabanninta Mr. Negas Gwanji ya bayyana. Ya ce sun yi mamaki da hurucin EFCC domin wannan itace shekarar farko da sunansu ya fita.
Ga cikakken rahoto daga Umar Faruk Musa.