Wani kamfanin tsaro da ke London mai suna AKE ya ce mafasan tekun sun kai harin ne kan wani jirgin ruwa mai dauke da tutar Amurka mai suna C-Retriever a jiya Laraba su ka sace keftin din jirgin da babban injiniyan.
Ba a sami bayanai nan da nan game da ko su waye Amurkawan ba, kuma nan dake babu wanda ya dau alhakin kai harin.
Kungiyar Ma’abuta Harkar Sufurin ruwa ta yi gargadin cewa akwai karuwar fashi da makami a mashigar ruwan Guinea da ke yammacin Afirka. Kungiyar ta ce kafin yau Alhamis, an sami rahotonnin aikata fashi daura da gabar Nijeriya a wannan shekarar, ciki har da garkuwa da mutane sau biyu.