ABUJA, NIGERIA - Sun ce illa dai ana kokarin karfafawa ‘yan kasa da su rika amfani da hanyoyin yanar gizo wato electronic channels wajen samun biyan bukata ne don rage yawan tsabar kudin dake zirga-zirga a cikin kasar.
Babban Bankin Najeriya CBN dai ya ce kudaden da ke zirga-zirga a kasar sun kai Naira tiriliyan uku da biliyan 690 a watan Fabrairun daya gabata wanda shi ne adadi dake zirga-zirga mafi yawa a tarihin kasar.
Alkalumman da suka bayyana haka bayan taron kwamitin manufofin kudin bankin wato MPC wanda aka sanar a ranar talata 26 ga watan Maris da muke ciki.
‘Yan Najeriya daga sassa daban daban sun yi ta korafi dai a kan takaita adadin kudin da zasu iya cira a cikin banki ko a ATM kamar yadda wani ‘dan kasa, Abdulaziz Mala ya ce ya je cire kudi kuma dubu 5 kawai ya iya cira.
Saidai wani jigo a bankin Access ya shaida wa Muryar Amurka ta wayar tarho cewa takaita iya kudin da mai asusu zai iya cira abu ne na bai daya a dukka bankuna ne kuma wani sashi ba zai iya kayyade yawan kudin da za’a iya cira ya banbanta da na sauran ba.
Yana mai cewa mutum zai iya cire Naira dubu 20 sau hudu a machine daya kuma matakin rage tsabar kudi da za’a iya cira baya rasa nasaba da kokarin rage yawan kudin dake zirga-zirga a cikin kasa wanda ya samo asali tun lokacin sauya launin kudi.
A wani bangare kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum Suleiman Hashim ya bayyana cewa bankin CBN karkashin Gwamna Olayemi Cardoso ya dora a kan dokar nan na rage yawan tsabar kudi dake cikin kasar ne saboda adadin dake yawo shi ne mafi girma a tarihin kasar.
Alkaluman kididdiga na baya-bayan nan dai sun yi nuni da cewa an sami kari a adadin Naira dake zirga-zirga a cikin kasar da kaso 1.8 cikin 100 na wata-wata daga Naira tiriliyan 3.65 da aka sanar a watan Janairun shekarar 2024 da muke ciki.
Idan ana iya tunawa tun bayan batun sauya launin kudi ake fama da matsalar adadin yawan kudi da mutane za su iya cira a cikin asusunsu na banki lamarin da wasu 'yan kasuwa ke korafe-korafe a kan wanda har yanzu akwai mutane masu dimbin yawa da ba sa amfani da hanyoyin yanar gizo wato electronic channels wajen hada-hadar kudinsu na yau da kullum.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:
Dandalin Mu Tattauna