Manajan Bankin First Bank, Alhaji Mu'azu, yace yanzu haka bai zai iya cewa ga wata fa'ida dangane da matakin rage darajar Naira da babban Bankin Najeriya ya bayyana ranar talata ba.
Babban Bankin wanda ya bayyana wannan mataki sakamkon faduwar farashin mai a kasuwannin duniya, ya kuma kara kudin ruwa da bankuna zasu karba daga masu amsar rance.
Alhaji Mu'azu yace daya daga cikin matsaloli da matakin zai janyo shine hauhawar farashin kaya, saboda galibin abunda Najeriya take amfani dashi sai an shigo dashi daga kasashen waje, domin faduwar darajar Naira hakan zai tilasta kayan suyi tsada.
Manajan Bankin yace banda jama'a, hatta masana'antu da kamfanoni, suma wannan mataki zai shafi kayayyaki da suke sarrafawa domin suma suna dogaro da kayayyaki daga kasashen waje, wajen tafiyarda ayyukansu.
Ga karin bayani.