Kungiyar Izalatil Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta tura agajin kayayyakin masarufi har na Naira miliyan 25 zuwa yankin arewa maso gabashin Najeriya domin agazawa mutanen da suka tagayyara a sanadin hare-haren 'yan Boko Haram.
Za a rarraba wadannan kayayyakin ne ga dukkan mutane ba tare da yin la'akari da addini ko akidarsu ba.
Shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce aikin taimako ya zamo wajibi a saboda muhimmancinsa, yana mai misali da yadda masu aikata zunubi ke iya shiga aljanna a saboda nuna halin jinkai ga wadanda ke cikin bukata.