Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Kano Ya Soma Kefen Neman Kuri'un Wakilai da Zasu Fitar da Gwani


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso.
Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso.

Kasancewar jam'iyyar APC bata cimma matsaya ba akan sulhun da ta shiga tsakanin 'yan takararta hudu yanzu 'yan takaran sun soma rangadin neman kuri'un wakilan da zasu yi zaben fidda gwani

Kwanaki biyu bayan zuwan Abubakar Atiku jihar Kebbi shi ma gwamnan jihar Kano Dr. Musa Rabiu Kwankwaso ya ziyarci jihar.

Gwamnan ya yiwa daruruwan magoya bayan jam'iyyar jawabi a sakatariyar ta APC dake Birnin Kebbi.

Ya kira masu zaben dan takarar shugaban kasa su yiwa jam'iyyar APC gata su zabi wanda Bahaushe ke cewa karen bana maganin zomon bana.

Muryar Amurka ta tambayi gwamnan na Kano akan inda aka kwana akan batun sulhu. Yace yawan 'yan takara da karfinsu shi ne karfin jam'iyya. Wata jam'iyyar ma bata da dan takarar shugaban kasa ko daya. Kuma ba zata samu ba domin bata da karfin samun dan takarar.

Yace ba zasu samu matsala ba domin dukansu masu hankali ne. Yace zasu bada dama su yi sulhu idan kuma bai yiwu ba zasu bar wakilai su fidda gwani. Duk wanda aka zaba shi ke nan.

Jam'iyyar APC reshen Kebbi ta nuna alamun marawa gwamnan baya musamman a matsayinsa na matashi. Sani Zauro Hukuma babban jigo ne a jam'iyyar. Yace duk inda ake akwai baba, akwai kanin baba akwai kuma da. Buhari shi ne baba. Atiku Abubakar shi ne kanin baba kana gwamna Kwankwaso shi ne dan baba. Yakamata su bar ma dansu. Idan suna son gaskiya su bada shawara a bar ma da, wato Kwankwaso domin shi biya masu bukata.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG