Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayin Wasu "Yan Mata Akan Amfani Da Turare Tsakanin Samari Da 'Yan Mata


Masu iya Magana sun ce idan an bi ta barawo to ya kamata abi ta mai bin sawu, a yayin da samari suka bayyana ra’ayoyin su dangane da tasirin turare a wajan ‘yan mata da kuma dalilin hakan, dandalin voa ya sami zantawa da wasu ‘yan mata inda suka bayyana mana nasu ra’ayoyin.

Kodashike yawanci samari sun ce yawancin ‘yan mata na anfani da turare ne saboda yanayin halittar jikinsu, su kuma ‘yan matan cewa suka yi lallai tsabta ce da kuma yanayi na son kwalliya da kowace mace ke da dashi yasa suke mu’amula da turare.

Daya daga cikin ‘yan matan sun bayyan mana cewar a lokacin da muke hirar nan da su, bai kai minti goma ba da suka gama shan azabar wari daga wasu fasinjoji da suka shigo mota guda daga inda suka fito. Sun kara da cewa a zahirin gaskiya da wuya ka gamu da mace mai wari haka, a cewar su idan ka hada mata goma da wuya ka sami guda biyu masu warin jiki amma maza abin ba a cewa komi.

Saurari cikakkiyar hirar a nan..Dandalin voa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG