Kim ya yi magana ne a wani taron manema labarai na ba saban ba, bayan ganawarsa da shugaba Vladimir Putin a Pyongyang, inda ya bayyana rattaba hannu kan "cikakkar huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare" wanda shugaban na Rasha ya ce ya hada da abubuwan kariya.
"Yarjejeniyar hadin gwiwa da aka rattaba hannu a kai a yau ta tanadi abubuwan da su ka hada da taimakon juna a yayin da ake kai wa daya daga cikin bangarorin wannan yarjejeniya hari," in ji Putin, wanda ya kai ziyararsa ta farko a Koriya ta Arewa cikin shekaru 24.
Ziyarar ta Putin mai yiyuwa ta sake fasalin alakar Rasha da Koriya ta Arewa tsawon shekaru da dama a daidai lokacin da dukkansu ke fuskantar wariya daga sauran kasashe, Seoul da Washington dai sun sanya ido sosai da kuma nuna damuwa akan wannan dangantakarsu ta soji.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna