Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pena Nieto Ya Yi Allah Wadai Da Kalaman Trump Na Gina Katanga


President Barack Obama, right, meets with Mexican President Enrique Pena Nieto, left, in the Oval Office of the White House in Washington, July 22, 2016.
President Barack Obama, right, meets with Mexican President Enrique Pena Nieto, left, in the Oval Office of the White House in Washington, July 22, 2016.

Kwana guda bayan da dan takarar jam’iyar Republican, Donald Trump, ya sha alwashin gina Katanga tsakanin Amurka da Mexico, shugaban kasar Mexicon, Enrique Pena Nieto, na ziyara a Amurkan a yau Juma’a.

Wannan ita ziyarar Pena Nieto ta farko tun bayan wacce ya kawo Fadar White a watan Janairu, wacce ita ce ziyarar shi ta farko.

Pena Nieto ya bayyana cewa kalaman Trump na cewa ‘yan MexicoRepublican na safarar kwayoyi da aikata manyan laifuka da yin fyade a Amurka, ya gurgunta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaban na Mexico ya soke wannan matsaya ta Trump, amma ya ce a shirye ya ke ya yi aiki da duk wanda zai gaji Obama.

Ana sa ran wannan ziyara, wacce aka sanar da ita a cikin wannan mako, za ta dora akan tattaunawar da kasashen biyu suka fara a taron kolin shugabannin kasashen arewacin Amurka suka yi a Ottawa kasa da wata guda da ya gabata.

XS
SM
MD
LG