Cleveland-Alhamis din nan ne ake sa ran dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump zai yi jawabi na amsa zama dan takara, a kuma dai dai lokacinda ake ci gaba da magana kan jawabin da tsohon abokin takararsa Senata Ted Cruz ya gabatar a daren ranar Laraba.
'Yan jam'iyya da magoya bayan Donald Trump, sun sa rai Ted Cruz zai bayyana goyon bayansa karara ga Donald Trump a cikin jawabinsa .Maimakon haka sai ya shawarci 'yan jam'iyyar su bi tunaninsu, inda ra'ayinsu ya karkata su yi can. Masu sharhi suna ganin yana gaya musu cewa ba dole bane su zabi Donald ba.
Ana sa ran cewa yau dai komi zai kasance cikin tsanaki, saboda ba wani cikin masu yin jawabai da ake tsoron zai furta wani abu dai zai janyo rigima ba.
Masu sharhi suna cewa illar maganar itace kara rarraba kawuna a dai dai lokacinda jam'iyyar take neman hada kai saboda ta tunkari jam'iyyar Democrat da Hillary Clinton.