Jam’iyyar PDP mai mulkin Nijeriya na cigaba da maida martani kan ficewar da babban jigonta tsohon Shugaban Nijeriya Chief Olusegun Obasanjo ya yi a fusace.
Na baya-bayan nan da ya maida martani shi ne Sakataren Kwamitin Zartaswa na jam’iyyar PDP Sanata Walid Jibrin, wanda ya ce sam su fa ficewar Obasanjo daga jam’iyyarsu ba ta dada su da kasa ba. Ya ce ganin yadda Obasanjo ya ba da umurnin a yaga katinsa ta shaidar zama dan jam’iyyar PDP a bainar jama’a, wannan na nuna rashin dattako da rashin mutunci daga bangarensa. Ya ce sam Obasanjo bai bi ka’idar ficewa daga jam’iyya ba saboda akwai ka’idar shiga da kuma fita jam’iyya. Ya ce ya kamata a ce Obasanjo ya je mazabarsa (Ward nasa) ya mika katin amma ba ya tara masu ra’ayinsa sannan ya fice tare da sa a yaga katinsa na jam’iyya ba.
Da Aliyu Mustapha na Sashen Hausa ya tambaye Mr. Jibrin ko Obasanjo ya zama masu kaya ne dama, sai ya ce ai Obasanjo ya zama masu abin da ma ya zarce kaya. Y ace fitar Obasanjo daga jam’iyyar PDP it ace alheri a garesu a maimakon irin fitinar da ya ce tsohon Shugaban Nijeriya din ke haddasa masu. Y ace ai Obasanjo ne ya kawo tsohon Shugaban Nijeriya Musa ‘Yar’aduwa, sannan ya kuma zo daga baya ya na ta kiran ‘Yar’aduwa ya sauka daga mulkin.
Da Aliyu ya tambayi Sanata Jibrin abin da ya ke jin shi ya sa Obasanjo ficewa daga jam’iyyar PDP din, sai ya ce ai babu jam’iyyar da ba ta da irin nata matsalolin. To amma da matsalolin PDP su ka ta’azzara Obasanjo bai nuna cewa shi dattijon PDP ba ne. Game da zargin wai Obasanjo ya taka rawa wajen matsalar zabe mai zuwa don a kafa gwamnatin rikon kwarya wadda shi zai shugabanta, sai Jibrin y ace shi bai san da wannan labarin ba.