Majalisar tace ta koresu ne saboda canza sheka daga jam'iyyar PDP zuwa ta adawa, wato APC da suka yi.
Wadanda aka kora su ne Bashir Isa Loko Goma mai wakiltar karamar hukumar Wushishi da Nazir Abdullahi daga karamar hukumar Rijau.
Barrister Adamu Usman shugaban majalisar dokokin ya bayyana dalilan daukan matakin korar mutanen biyu. Yace kundun tsarin mulki ya bayyana cewa duk dan majalisa da ya canza sheka ba tare da an samu baraka a jam'iyyarsa ba ko rarrabuwan kawuna to kamata yayi ya bar kujerarsa.
Majalisar ta cigaba da zama a cikin wani hali na hayaniya bayan bayyana korarsu domin ba'a basu daman mayarda martani ba.
Mutanen da aka kora sun sha alwashin kalubalantar korar a kotu. Bashir Loko Goma yace sauransu watanni uku su gama wa'adinsu sabili da haka shi bai ga abun da zai tsinana ba cikin sauran lokacin. Amma ya ce nan da nan zai garzaya kotu.
Shi kuma Nazir Abdullahi yace abun da aka yi masu misali ne na cin zarafi da take hakin bil Adam. Yace dokar kasa ta ba kowa aka zama hurumin canzawa zuwa wata jam'yya idan akwai rikici a jam'iyyarsu.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar Nurudeen Umar yace korar bata cikin tsari. Yayi misali da kakakin majalisar wakilai na tarayya wanda ya canza sheka daga PDP zuwa APC duk da shi ne shugaban majalisar. Kuma har yanzu yana shugabancin majalisar.
Tuni jam'iyyar APC a jihar ta bayyana matsayinta akan korar mabobin. Mr. Jonathan Batsa kakakin jam'iyyar a jihar yace matakin da zasu dauka daya ne. Zasu je kotu ba tare da bata lokaci ba. Kotu ce zata warware matsalar.
A wata sabuwa kuma yau shugaban majalisar Barrister Adamu Usman zai karbi ragamar mulkin jihar daga gwamna Babangida Aliyu a matsayin gwamnan riko domin shi gwamnan zashi yin aikin umura a kasar Saudiya. To saidai matakin ya jawo ayar tambaya akan makomar mataimakin gwamnan Ahmed Musa Ibeto wanda shi ma ya canza sheka zuwa jam'iyyar APC.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.