Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PAKISTAN: Wani dan kunar bakin wake ya halaka akalla mutane 12


Wurin da bam ya tashi a Pakistan yau Talata
Wurin da bam ya tashi a Pakistan yau Talata

Jami’ai a arewa maso yammacin Pakistan sun ce ana zaton wan harin kunar bakin wake yau Talata ya hallaka akalla mutane 12 wasu da dama kuma sun raunata. Yawancin wadanda abin ya rutsa da su jami’an tsaro ne.

‘Yan kungiyar Taliban sun dauki alhakin kai harin .

Shaidun gani da ido sun ce maharin akan babur ya kai harin inda ya afkawa wani shingen tsaro wanda ya raba birnin Pashewar da gundumar Khyber ta kabilu masu ‘yancin cin gashin kansu kadaran-kadahan, masu fama da tashin-tashina kuma.

Ma’aikatan agaji da jami’an yankin sun ce wani babban jami’in ‘yansanda na wannan kabila da kuma wani dan jaradar garin na cikin wadanda suka rasa rayukansu.

Fashewar bom din ta yi ratarata da motoci da yawa da baburan da aka ajiye kusa da wajen da jami’an tsaron suke

Khyber ta kasance daya daga cikin manyan hanyoyin kasuwanci tsakanin Pakistan da Afghanistan.

Wannan wurin na kabilar ta Pakistan, wuri ne da mayakan yankin da na kasashen ketare su ka sha kai hare-hare a wajen iyakar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG