Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Pakistan Ya Gana da Shugaban Amurka


Firayim Ministan Pakistan Nawaz Sheriff
Firayim Ministan Pakistan Nawaz Sheriff

Shugaban Amurka Barack Obama yayi maraba da Firaministan Pakistan Nawaz Sheriff a fadarsa ta White House a jiya Alhamis.

Tare da sabunta alkawarin karfafa dangantaka tsakanin kasashen ta yadda hakan zai zama kwarin gwiwa game da wanzuwar zaman lafiyar Afghanistan.

Shugabannin biyu sun bayyana daga ofishin shugaban kasa da ake kira Oval Office inda suka gama tattaunawar tare da kin bayyana tsawon lokacin dadadden shirin zaman lafiya.

Maimakon ma haka sai suka fito da zayyana yadda kasashen biyu za su inganta harkar kasuwanci da tsaftacacce makamashi da ilimin mata.

A wata gajeriyar hira kafin su shiga tattaunawar, Shugaba Obama ya bayyana cewa, dama Amurka da Pakistan sun dade da abota akan al’amura da dama.

Ya kara da cewa, “ina fatan wannan dangantaka za ta dore don zurfafa tsare-tsaren gudu da tsira tare.

Shima Nawaz din ya bayyana cewa, “Kawancen Amurka da Paskistan ya haura shekaru 70. Sannan kuma muradun a bunkasa wannan kawance.”

Obama ya bayyana yadda suke son kwashe sojojin Amurka daga Pakistan, amma dole za su bar wasu na dan wani lokaci saboda kasar na da matsalar dadaito.

XS
SM
MD
LG