Kafofin soja a kasar Pakistan sunce jiya juma'a aka kashe wasu yan yakin sa kai guda biyu da aka samu da laifi, a yayinda gwamnatin kasar ta zafafa maida martani ga kisan kiyashin da aka yiwa kimamin mutane dari da arba'in yawancinsu yaran makaranta a Pashewar.
Jami'ai sunce Ageel wanda kuma ake cewa Dr Usman da kuma Arshad Mahmood, an rataye su a gidan yarin Faisalbad. Wata kotun soja ce, ta samu mutane biyu da laifin kula makarkashiyar kai hare hare akan hedikwatar soja, da yunkurin yiwa tsohon shugaban kasar Pervez Musharraf kisan gila da kuma mumunar harin da suka kaiwa yan wasan gora na kasar Sri Lanka da ake cewa Cricket da turanci, wadanda ke ziyara.
Haka kuma, hafsan sojojin kasar Raheel Sharif ya sanya hannu akan dokar kashe karin yan yakin sa kai guda hudu, kuma nan bada jimawa ba suma za'a kashe su.
Kungiyar Amnesty da cibiyarta ke birnin London da kungiyar dake hankoron kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch da cibiyar ta ke nan Amirka duk sunyi Allah wadai da shawarar da shugaba Sharif ya yanke na maido da dokar hukuncin kisa a kasar. Kungiyar Amnesty tace wannan martani ne da ba zai magance matsalar ba.
A yayinda Pakistan ta shiga rana ta uku na zaman makoki, sojoji sunyi kwantar bauna suka kashe akalla yan yakin sa kai hamin a yankin Kyber kusa da kan iyakar kasar da Afghanistan.
An kashe wasu karin yan yakin sa kai guda takwas a lardin Baluchistan dake kudu maso yammacin kasar ciki harda wani kwamandan yan kungiyar Taliban.