Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Libya Suna Neman Tallafin Kudi Daga Manyan kasashe Dake...


Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton daga tsakiya take tattaunawa da ministan harkokin wajen Jordan daga hagu,da na hadaddiyar daular larabawa daga hanun dama.
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton daga tsakiya take tattaunawa da ministan harkokin wajen Jordan daga hagu,da na hadaddiyar daular larabawa daga hanun dama.

‘Yantawayen kasar Libya na can suna neman milyoyin daloli daga jagabannin kasashen dake halartar taron da ake gudanarwa a Haddadiyar Daular Larabawa don shata makomar Libya bayan an kaswarda shugabanta na yanzu, Muammar Ghadafi.

‘Yantawayen kasar Libya na can suna neman milyoyin daloli daga jagabannin kasashen dake halartar taron da ake gudanarwa a Haddadiyar Daular Larabawa don shata makomar Libya bayan an kawarda shugabanta na yanzu, Muammar Ghadafi.

A wajen wannan taron da ake a birnin Abu Dhabi, kasar Italiya, wacce tayi wa Libya mulkin mallaka, tayi alkawarin bada tarbaccen Dala milyan 600, koda yake tallafin zai hada da rance ga ‘yantawayen.

kampanin dillacin labaran Associated Press yace ita ma gwamnatin shugaba Obama na Amurka tayi alkawarin kara yawan tallafin agajin da take baiwa Libya din zuwa Dala milyan 26 da dubu 500. Sakatariyar Harakokin Wajen Amurka Hilary Clinton ta gayawa mahalarta taron cewa “kwannakin Ghadafi sun kare.”

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG