Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya caccaki sauye-sauyen Shugaba Bola Tinubu inda ya bayyanasu da marasa kyau.
A cewar sanarwar da hadiminsa a kan harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi ya fitar, Obasanjo yayi zargin cewar a halin yanzu Najeriya na cikin wani kangin gwamnati kuma yanayin bashi da kyau ko kadan.
An ruwaito tsohon shugaban kasar na fadin haka ne yayin gabatar da jawabin bude taro a dandalin koyar da shugabanci na Chinua Achebe, a sabuwar jami’ar Yale dake New Heaven Connecticut, a kasar Amurka.
A jawabin nasa mai taken “gazawar shugabanci da kangin gwamnati”, Obasanjo ya bayyana halin da Najeriya ke ciki da mummuna.
Tsohon shugaban kasar ya kuma yi zargin cewa an tabbatar da matakin gazawar Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmad Tinubu, kuma komai ya bayyana karara ga mutane masu gaskiya su gani.”
Sai dai, a wani martani da ya mayar nan take ta hanyar jerin sakonnin Twitter, mashawarcin Shugaba Tinubu a kan hulda da jama’a, Sunday Dare, yace tsohon shugaban kasa Obasanjo bashi da mutuncin da zai soki gwamnatin Bola Tinubu.
Dare ya kara da cewa suna nan sun tattara dukkanin soki-burutsun da ya gabatar a matsayin hujjoji.
Dare ya kuma bayyana gwamnatin Obasanjo da wacce ta yi kwarin suna a cin hanci da rashawa, inda ya kafa hujja da aikin samar da lantarki na dala biliyan 16 da bai haifar da mai ido ba wanda ya sha suka.
“Dukkaninmu muna sane da abinda ya faru karkashin mulkinsa dama yadda aka yi, har zuwa yanzu, babu cikakken bayani a kan yadda aka kashe dala biliyan 16 wajen samar da megawatt ta duhu a fadin Najeriya.”
“Kamata yayi ya nemi gafarar ‘yan Najeriya saboda gazawa wajen samar da kayayyakin more rayuwa da Najeriya ke bukata domin samun ci gaba,” a cewar Dare.
Dandalin Mu Tattauna