Taron kwararrun zai duba hanyar inganta wutar lantarki domin bunkasa masana'antun nahiyar. Ta yin hakan su kuma masana'antu su samar ma 'yan kasa ayyukan yi musamman matasa.
Duk da biliyoyin nera da gwamnatocin baya suka kashe a Najeriya wajen inganta wutar lantarki amma har yanzu 'yan Najeriya na lalube cikin duhu da tocila ko anfani da injinan janareta saboda gudanar da sana'o'i da kuma harkokin cikin gida.
Masana sun ce lamarin da sake. Malam Boli Kogi Gado ministan wutar lantarki na jamhuriyar Nijar yace ya kamata hukumomi da kamfanoni sun san yadda zasu ciwo kan karancin wuta da makamashi.
Masana da kamfanonin duniya a wajen taron sun fi maida hankali ne akan Najeriya kasar da ka iya saka dimbin jari a harkokin wuta da makamashi. Malam Alkali Ahmad na hukumar IAEA mai kula da makamashin nukiliya yace dole ne Najeriya ta karkata wajen yin anfani da makamashin nukiliya domin samun wuta mai araha bisa ga la'akari da cewa kasar nada al'umma mai dimbin yawa kuma nan da shekaru ashirin zasu ninka kana ita Najeriya din zata zama kasa mafi karfin arziki a nahiyar Afirka.
Malam Gado minista a jamhuriyar Nijar da yake magana akan anfani da makamashin nukiliya wajen samun wutar lantarki yace kamfanoni su ne suka san inda ya dace a gina nukiliya. Su ne suka san ina ne ake da man fetur ko gawayi, iska ko rana. Yace duk wadannan ana iya yin anfani dasu domin a samu wutar lantarki.
Shi ma tsohon ministan wutar lantarki na Najeriya Farfasa Pat Nnaji cewa yayi akwai bukatar maida hankali da aiki tukuru domin fitar da Najeriya daga duhun wutar lantarki da take ciki a halin yanzu.
Ga rahoton Babangida Jibril.