WASHINGTON DC - Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajero ya bayyana tayin karin tsakanin kaso 25 zuwa 35 cikin 100 na albashin ma'aikatan gwamnatin Najeriya da gwamnatin tarayya tayi a jiya Talata a matsayin makirci.
"Akwai wani abu mai kama da makirci a sanarwar kasancewar babu batun karin albashi a cikin sanarwar gwamnatin," a cewar Ajero a cikin wani shirin tashar talabijin ta Channels na sassafe me suna "Sunrise Daily" na yau Laraba, a daidai lokacin da ma'aikata a fadin duniya ke gudanar da shagulgulan bikin ranar ma'aikata ta bana.
"Gwamnatin tarayya ta hanun majalisar dokokin kasa tayi dokoki akan batun. Amma yanzu sai muka ga batun yabi iska saboda gwamnatin tarayyar ta gaza sake kiran taron da aka dage zamansa a baya".
A baya cikin watan Janairun daya gabata, gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti mai kusurwa 3 wanda ya kunshi wakilai 37 akan mafi karancin albashi na kasa tare da umartarsa ya bada shawarwari akan mafi karancin albashi ga Najeriya, saidai har yanzu gwamnatin ta gaza aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar.
A jiya Talata, mai magana da yawun Hukumar Kayyade Albashi ta Najeriya (NSIWC), Emmanuel Njoku, yace karin albashin ya fara aiki tun daga ranar 1 ga watan Janairun daya gabata.
Saidai, Karamar Ministar Kwadago Nkeruka Onyejeocha tace, " duk da cewar kwamitin mafi karancin albashi nan mai kusurwa 3 bai kammala tattaunawa akan batun ba, ma'aikata ba zasu yi asarar komai ba kasancewar sabon mafi karancin albashi zai soma aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Mayun da muke ciki.
Ministar ta bayyana hakan ne a yau Laraba a jawabinta ga ma'aikatan Najeriya yayin bikin Ranar Ma'aikata ta duniya a Abuja.
A mabambantan lokuta, kungiyar kwadago ta NLC da takwararta ta TUC sun bukaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta hanzarta kara albashin ma'aikata, kuma a baya-bayan nan kungiyoyin sun bukaci a biya naira dubu 615 a matsayin mafi karancin albashi domin dacewa da halin matsin tattalin arzikin da tsadar rayuwa da ake fama dasu a Najeriya a halin yanzu.
Dandalin Mu Tattauna