A Yau Laraba, ma'aikatan Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na sauran duniya wajen yin shagulgulan bikin zagayowar ranar ma'aikata ta duniya mai lakabin "May Day" a turance.
Bikin ranar ma'aikata na bana shine na farko karkashin mulkin Shugaba Kasa Bola Tinubu wanda aka rantsar a ranar 29 ga watan mayun shekarar 2023.
Tuni dai, gwamnatin tarayya ta ayyana Laraba 1 ga watan Mayun da muke ciki ta zama ranar hutu domin gudanar da shagulgulan bikin ranar ma'aikata ta bana a fadin Najeriya.
An ruwaito sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Gidan Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ya fitar na cewar, "a bisa dacewa da taken bikin na bana, wanda ya maida hankali akan tabbatar da kiyaye afkuwar hatsari da lafiyar ma'aikata a wurin aiki a yanayi mai sauyawa, ina son in bayyana cewar gwamnatin tarayya na nan akan kudirinta na bada fifiko akan kiyaye lafiya da walwalar dukkanin al'ummar Najeriya”
Ministan ya cigaba da cewar, "bari in jaddada kudirin Shugaban Kasa na samar da kyakkyawan yanayin gudanar da ayyuka, inda kowane ma'aikaci zai nuna kwazo tare da bada kyakkyawar gudunmowa wajen gina kasa".
'Yan Najeriya sun gudanar da bikin Ranar Ma'aikata ta Duniya na bana cikin dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai a daidai lokacin da matsalar karancin mai ke kara kamari a fadin kasar.
Duk da tabbacin da babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, ya bayar na magance matsalar, ana cigaba da ganin dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai yau fiye da mako guda.
sabuwar matsalar karancin man ta kassara harkokin tattalin arziki a fadin kasar kasancewar a ko'ina a fadin Najeriya al'umma na bin dogayen layuka a gidajen mai.
A yayin da wasu masu ababen hawan suka yi sa'ar sayen litar man a wasu gidajen man a tsakanin Naira 700 zuwa 1200 bayan shan gwagwarmaya, wasu basu samu hakan ba sakamakon kasancewar galibin gidajen man a rufe, a bisa uzurin rashin wadatar man.
Sakamakon matsalar karancin man fetur din 'yan bumburutu na sayar da litarsa akan abinda ya kai naira dubu 2 a wasu jihohin Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna