Daya ga watan mayu rana ce da aka ware a duk shekara a matsayin Ranar Ma’aikata ta Duniya domin yin waiwaye adon tafiya akan nasarori da ma’aikata suka samu da kuma matsalolin ko kalubalen da suka fuskanta a kasashe daban daban.
Saidai ranar tazo wa ma’aikatan Nijar daidai lokacin da kasar ke fama da hauhawar farashin kayan masarufi, lamarin da yassa ma’aikatan kokawa kan yadda albashi baya iya biya musu bukatu na yau da kullum.
Kungiyoyin Ma’aikatan sun bukaci gwamnatin Nijar da ta kawo karshen kwantiragi domin inganta harkokin aiki a kasar.
Ma’aikatan a karkashin kungiyoyin su sun fito inda suka gudanar da jerin gwano a gaban gwamnonin jihohi kamar yadda aka saba a kowace shekara domin mika kokensu.
Hukumomi sun karbi koken ma’aikatan tareda bayyana musu cewa zasu zauna kan teburin tattaunawa.
A saurai cikakken rahoton Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna