Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NLC: Kungiyar Kwadago Ta Gombe Ta Jinjinawa Gwamnan Jihar


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

Kungiyar kwadago ta jihar Gombe ta jinjinawa gwamnan jihar Ibrahim Hassan Dankwambo

Kungiyar ta yaba masa ne bisa ga jajircewar da yayi na ganin cewa an biya albashin ma'aikata a kan lokaci kuma masu karbar kudin fansho ba'a barsu a baya ba.

Tun da farko kuwa sai da sai da gwamnan yace ma'aikatan jihar basa binsa bashin albashi na ko kwandala. Yace cimma wannan matsayin ba wata hikima ba ce babba saidai yin tattali. Yace idan aka yi la'akari da yadda kudade ke shigowa daga tarayya da kuma cikin gida idan ba'a yi hattara ba nan gaba za'a samu matsala. Yace ya fahimci hakan kuma ya fara daukan matakai domin kada ya shiga matsala. Yace sun fara duba wasu hanyoyi da zasu samu kudaden shiga.

Dangane da manyan ayyukan da gwamnan yayi can baya lokacin da akwai wadata gwamnan yace a wannan yanayin da suke ciki zai mayar da hankali ne akan kammala ayyukan da suka soma. Sai sun gamasu ne zasu soma tunanen wasu sabbi.

Shugaban kungiyar kwadago reshen Gombe Haruna Kamara yace gwamnan jihar Dankwambo ya yi fice game da biyan ma'aikata.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG