Ita gwamnatin ta dakatar da ma'aikata fiye da dubu uku musamman wadanda aka dauka aiki daga shekarar 2012 zuwa 2015.
Wanan matakin zai shafi ma'aikata fiye da dubu uku bayan da ta kammala tantance wadanda aka dauka aiki a shekarun da ta ambata a cikin sanarwar da ta fitar.
Ma'aikatan jihar da aka zanta dasu sun ce abun bakin ciki ne ya addabesu da kuma jihar gaba daya. Sun ce wasunsu har an basu aiki na din-din-din da zai kai ga fansho.Mutanen sun ce ba haka suka yi fata ba. Suna fatan shi sabon gwamnan zai cigaba daga inda aka tsaya.
Tuni kungiyar kwadagon Najeriya reshen Taraba ta kirawo taron gaggawa dangane da lamarin. A wurin taron ta yanke shawarar baiwa gwamnatin kwana uku kacal da ta yanje matakin da ta dauka.
Kwamred Peter Gambo shugaban kungiyar kwadagon yace bayan kwana uku idan gwamnati bata janye dakatar da ma'aikatan ba zasu rufe ayyukan gwamnati. Yace ba'a korar ma'akata ba tare da aikata wani laifi ba.
A cikin martanin da gwamnatin ta mayar sakataren yada labaran gwamnan Alhaji Hassan Mijinyawa yace gwamnati ta dauki matakin ne bisa ga abun da ta kira tsarkake ma'aikatan jihar. Yace idan za'a dauki ma'aikata dole ne a sanarda kowa. Amma su wadannan daga bangare daya kawai aka daukosu lamarin da yace ba'a yi adalci ba. Yace dole ne gwamnati ta dakatar dasu, ta duba idan kuma za'a sake sai a sake.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.