Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Kama Wani Shugaban 'Yan Bindiga Da Ake Nema Ruwa A Jallo A Najeriya


Yan bindiga da aka kama
Yan bindiga da aka kama

An kama wani shugaban ‘yan fashi da makami a Najeriya da ake nema ruwa a jallo da yin garkuwa da jama’a tare da mutanensa 65 a kudancin Nijar, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar.

Gwamnan yankin Issoufou Mamane ya shaida wa gidan talabijin na jama'a da yammacin Laraba cewa, "bayan kwanaki da dama da ake ta bin sa, a karshe mutanen mu sun kama shahararren (Kachalla) Baleri da wasu mutanensa."

Yan bindiga da aka kama
Yan bindiga da aka kama

Tashar talabijin ta bayyana wasu faifan bidiyo na wasu mutane goma sha biyu da aka daure da sarka da fuskar su a rufe suna zaune a kasa, ta na mai cewa an kama su yayin wani taron su inda su ke shirya kai hare-hare kan jami'an tsaro".

Gwamnan yankin Maradi ya ce Baleri daga jihar Zamfarar Najeriya yana lamba 40 a jerin sunayen sojojin Najeriya da ake nema ruwa a jallo.

Yan bindiga da aka kama
Yan bindiga da aka kama

A cewar gidan talabijin na jama'a, Baleri ya shiga cikin "hare-hare da dama inda aka zubar da jini a Najeriya", da kuma harin da aka kai a ranar 22 ga watan Fabrairu da ta gabata wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Nijar hudu daga bangaren yaki da ta'addanci da suka kama shi a ranar Laraba.

Yan bindiga da aka kama
Yan bindiga da aka kama

“Masu fyade ne, barayin shanu da kuma masu kashe mutane ba imani,” in ji mai shigar da kara na babbar kotun Maradi, Adam Adamou.

Dakarun sojojin kasashen biyu sun gudanar da ayyukan hadin gwiwa domin dakile tashe tashen hankula.

Sama da shekaru 10 dai, iyakar Najeriya da Nijar ta kasance maboyar kungiyoyin ‘yan bindiga wadanda ke sace fararen hula domin neman kudin fansa da kuma satar shanu.

~ AFP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG