Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lalata Asibitoci A Fadan Sudan Ya Jefa Majinyata Mawuyacin Hali


Yan gudun hijirar Sudan a Chadi.
Yan gudun hijirar Sudan a Chadi.

Yakin da ake gwabzawa a Sudan ya lalata asibitoci da kuma cibiyoyin kula da lafiya a kasar, kuma majinyatan da suka tsere daga rikicin na neman magani.

Yayin da ake fama da rashin tallafin jinya, wani mai harhada magunguna dan kasar Sudan da ya tsere daga Sudan a makonnin da suka gabata yana yin duk mai yiwuwa don taimakawa wasu ‘yan gudun hijira a wani sansani a makwabciyar kasar Chadi.

A watan daya da ya gabata, Mohammed Adam ya tattara irin magungunan da zai iya a lokacin da ya ji kungiyar Janjaweed, wata kungiyar da ta shahara wajen kashe fararen hula, na shirin kai hari garinsu na Tendelti a yammacin Darfur. Ya ce ya loda magungunan ne a kan keken doki, inda ya yi tafiya mai nisan kilomita ko makamancin haka ya tsallaka kan iyaka zuwa makwabciyar kasar Chadi.

Tun daga wannan lokacin, ya kafa wani kantin magani na wucin gadi a Koufroune, wurin 'yan gudun hijira inda kusan mutane 10,000 ke zaune.

Tun lokacin da rikicin Sudan ya fara a ranar 15 ga Afrilu, Chadi da kungiyoyin agaji sun yi ta kokawa wajen samar da isasshen abincin da 'yan gudun hijira za su ci. Agajin magani yana da karanci, a cewar 'yan gudun hijirar.

A cikin Sudan, tsarin kula da lafiya ya durkushe.

Wani faifan bidiyo na ya nuna wani asibiti a birnin Khartoum da fada ya kone kurmus. Wasu kuma a birnin an ce sun samu mummunar barna, tare da asibitoci a yammacin Darfur, inda ake gwabza kazamin fada.

Kungiyar likitoci masu zaman kansu ta Doctors Without Borders ta fada ranar Talata cewa an wawashe kayan aikinta, yayin da aka kashe ma'aikaci a cikin watan Afrilu a fadan. Ta ce kwasar ganima za ta haifar da sakamako na "rashin rai" ga al'ummar Sudan.

Ameir Eltom shine mataimakin sakatare-janar na kungiyar Likitocin Amurka ta Sudan. Ya ce kasancewar gwamnatin Sudan ba ta aiki saboda fadace-fadacen da ake yi, kungiyarsa na taimakawa wajen gudanar da ayyukan wasu asibitoci.

Tsagaita wuta na mako guda da aka fara ranar litinin ya kamata ya ba da damar wasu kayan agajin jinya shiga kasar.

Ya roki duk kungyoyi masu zaman kansu da kuma al'ummomin gida da su taimaka wa 'yan gudun hijirar saboda da gaske suna bukata. Ba su da wurin da za su kare kansu daga ruwan sama, wanda ke taimakawa wajen yada cututtuka. Ya kuma damu da yaduwar cutar kwalara, wacce za ta iya rikidewa zuwa annoba, wadda za ta zama bala'i.

Ya ce yana yin abin da zai iya, da dan abin da yake da shi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG