Yayin da a daya bangare tallafin irin wannan yunkuri ka iya bai wa magidanta damar cike gurbin cimakar da ake fuskanta sakamakon matsalaolin da suka lalata amfanin gonaki a damanar da ta gabata.
Bayanan mahukuntan Nijar sun tabbatar da cewa gardamar damanar a bana ta haddasa lalacewar a kalla kashi 50 daga cikin 100 na amfanin da aka yi hasashen samu lamarin da ya sa gwamnatin kasar daukan matakai da nufin tunkarar wannan al’amari kamar shirin sayar da cimaka akan farashi mai rahusa ko rarraba cimakar kyauta a wuraren da abin ya yi kamari.
Sai dai a wata hirar musamman da sarkin Dungas mai martaba Amadou Zakari ya ce yana ganin maida hankali wajen noman rani it ace hanya mafi a’ala a halin da ake ciki a yau.
A irin wannan lokaci matasa kan rika ficewa zuwa ci rani kasashen da ake daukansu a matsayin bakin haure saboda haka sarkin Dungas ya ce akwai bukatar kungiyoyi masu zaman kansu su shigo wannan lamari don ganin jama’a ta ci moriyar albarkatun ruwan da Allah ya horewa yankunan wannan kasa misali da karkarar da yake shugabanta.
Shugaban kungiyar matasa ta AJEPA Laouali Tsalha shi ma ya yi na’am da wannan shawara na cewa matakin zai taimaka wajen yaki da talauci da yaki da zuwan ciranin matasa sannan hanya ce ta samar da wadatar abinci a kasa.
Noman dama na kan gaba a ayyukan da mafi yawancin jama’ar Nijar ke dogaro a kansu saboda haka fannin ke da mahimmanci sosai wajen samar da wadatar cimaka a wannan kasa dake fama da kwararowar hamada da a daya gefe illolin canjin yanayi.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: