Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cin Hanci da Rashawa Sun Fi Yiwa Kasashen Afirka Kudu da Hamada Katutu


Transparency International
Transparency International

Binciken Transparency International na shekara shekara ya nuna cewa har yanzu cin hanci da rashawa na ci gaba da yiwa kasashen Afirka katutu, lamarin da ya hanasu ci gaba kamar yadda ya kamata

Kasashen Afrika, kudu da Hamada sun ci gaba da kasancewa kan gaba a jerin kasashen da cin hanci da rashawa ya yi katutu, bisa ga binciken da kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa da kasa “transparency International” take gudanarwa shekara shekara. Binciken ya nuna kasar Somaliya ita ce kashin bayan na tsawon shekaru goma sha biyu a jerin kasashen dake yaki da cin hanci da rashawa, bayanda cibiyar ta gudanar da bincike a kasashe dari da tamanin.

Binciken ya kuma gano cewa, sama da sulusin kasashen da aka gudanar da binciken basu sami makin da ya shige hamsin cikin dari ba, inda aka dauki arba’in da uku a matsayin madaidaicin maki. Galibin kasashen nahiyar Afrika basu wuce maki talatin da biyu cikin dari ba. Babu wata kasa a duniya da ta tabo samun dari bisa dari. Kasar Neitherland ce kan gaba a matsayin kasar da ba a cika samun matsalar cin hanci da rashawa ba, inda kasar ta sami maki tamanin da tara cikin dari, yayinda kasar Somalia ta sami maki tara.

Mai ba kungiyar sa ido kan yaki da cin hanci da rashawa ta kasa da kasa shawarwari ta shiyar Kudancin Afrika, Kate Muwoki tace, “galibin gwamnatocin Afrika basu daukar matakin shawo kan cin hanci da rashawa a yankin, ko da yake shugabannin nahiyar da dama sun dauki matakan sauya dabi’un al’umma.

Tace mai yiwuwa ne lamarin ya canza, kasancewa KTA da shugabannin manyan kasashen nahiyar da suka hada da shugabannin kasashe biyu da suka fi karfin tattalin arzikin a nahiyar, Najeriya da Afrika ta Kudu, sun bayyana niyarsu ta ba yaki da cin hanci da rashawa fifiko.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG