NIAMEY, NIGER - Yanayin da tsadar rayuwar da aka shiga a wani lokacin da ake fama da karancin kudi a hannun jama’a, kungiyar MDD, wato mata masu dubara, ta shirya taron gangami don bayyana wa duniya halin da aka shiga a Nijar sanadiyyar jerin takunkuman da aka kakaba wa kasar, inda aka fara fuskantar jinkirin biyan albashi inji su.
Dubban miliyoyin cefa mallakar gwamnatin Nijar da ke ajiye a bankin bankunan kasashen yammacin Afrika rainon Faransa ne aka bayyana cewa bankin na BCEAO na rike da su a tun daga washe garin juyin mulkin da soja suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum, dalilin kenan da ya sa matan kungiyar MMD suka yi tattaki a ranar Alhamis daga MJC Djado Sekou zuwa harabar ofishin bankin na BCEAO da ke tsakiyar birnin Yamai don nuna rashin amincewa da wannan mataki.
Domin jin matsayin BCEAO akan wannan al’amari Muryar Amurka ta tuntubi kungiyar SYNBANK ta hadin kan ma’aikatan bankuna wace ta hada wakilinmu da wani jami’in reshen bankin a nan Yamai, amma muka yi ta kira ta waya da kuma aika sakon text bai amsa ba.
Rike kudade da kadarorin gwamnatin Nijer na daga cikin jerin takunkumai 10 na fannin hada-hadar kudaden kasuwanci da na tattalin arziki da kungiyar UEMOA ta kakaba wa Nijar a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023, matakin da sannu a hankali illolinsa suka fara shafar al’amuran rayuwar jama’a na yau da kullum.
Tsaikon biyan albashin ma’aikata na daga cikin irin wadannan matsalolin, koda yake a cikin daren Alhamis an fara biyan albashi na watan Satumba a wasu bankuna a cewar rahotanni.
A wani yunkurin tunkarar kalubalen da ke da nasaba da takunkuman kasashen yammacin Afrika, majalissar CNSP ta bude gidauniyar tattara gudunmowar kudaden gudanar da al'amuran kasa.
Tuni kuma da wasu ‘yan Nijar mazauna ketare suka turo tasu gudunmawar kudi million sama da 100 na cefa, da nufin jaddada goyon baya ga sabbin shugabannin na mulkin soji.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna