Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Siyasan Jamhuriyar Nijar Na ci Gaba Da Nuna wa Juna Yatsa


Hagu zuwa Dama: Sakataren Hukumar raya Tabkin chadi, Sanusi I. Abdullahi; Shugaba Thomas Boni Yayi na Jamhuriyar Benin; shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya; shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar; shugaba Idris Deby na Chadi; wakilin shugaban Kamaru, minist
Hagu zuwa Dama: Sakataren Hukumar raya Tabkin chadi, Sanusi I. Abdullahi; Shugaba Thomas Boni Yayi na Jamhuriyar Benin; shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya; shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar; shugaba Idris Deby na Chadi; wakilin shugaban Kamaru, minist

Sanin kowa ne kwanan yan siyasa a jamhuriyar Niger , basu amince wa juna maimako sai suna kara rarraba kawunan a tsakanin su.

Wannan yasa kungiyoyin farar hula kamar yadda Mustafa Kadi ya shaidawa sashen Hausa na Muryar Amurka, kungiyoyin su na farar hula ta dauki nauyin aikin zama dasu waje guda domin su tattauna a tsakanin su.

Yin hakan zaisa a dubi kasar a daina son rai, domin sanin kowa ne a wannan lokacin na zabe idan ya samu, abinda yake da anfani shine a iya cewa kungiyoyi na siyasa sun zauna kan teburi guda kamar sun sa wa jarabawa ko kuma wata sanarwa hannu, wanda kowa zai amince cewa ayi zabe cikin kwanciyar hankali ayi zabe lami lafiya kuma ayi zabe da kowa da kowa ba cikin wariya ba.

Domin haka kungiyoyin sunce zasu kawo gudun mowa ta horas da yan siyasa, domin kwatanta musu abinda dokoki suka nuna, domin ya zamo kome za ayi a jamhuriyar Niger a iya cewa ya tsaya kan gaskiya, kowa yayi adalci, kana kowa yabi doka.

Kadi yace muddin ba ayi aiki da doka ba to anyi baya ba zane Kenan, yace don haka suke so duka kungiyoyin farar hula su kama hanya, guda

To sai dai da aka tambayi Mustafan ganin yadda jamiaan tsaro a Africa sukan rika marawa gwamnati maici baya ko suma sukan hada dasu wajen wayar musu da kai domin samun zabe nigari?, nan ko ga amsar da Mustafa Kadi ya bayar.

Ai bai yiyuwa ne ka ware jamiaan tsaro kamar sojoji ko yan sanda da dai sauran masu sa kayan sarki kace ba ayi dasu, yace duk aikin da kungiyar su zata yi sai tace a nemo wadannan masu sanye da kayan sarki asa su ciki.

Yace wata rana ma suna shirya nasu ne ma na musammam ko kuma suyi da kansu, yaci gaba da cewa yanzu haka akwai masu zuwa makaranta ta yan sanda suna horas dasu ta wannan fannin.

Yace wannan batu na harkar siyasa ko kuma zabe tunda ya shafi kowa, wannan yasa hatta sarakuna ma sukan sa su cikin wadan da ake horaswa, suma alkalai ba a barsu a baya ba, domin akwai wasun su sukan rika karanbani cikin harkan zabe suma ba a barin su wajen wannan horaswan.

Yaci gaba da cewa tunda wannan harka ta zabe ya shafi kowa to ya dace ace kowa a kwatanta masa cewa ga matsayin sa ga kuma inda bai kamata ya tsallaka ba.

Ga cikakkiyar hirar tasu

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG