Tun lokacin da ta zama jamahuriya shugabanninta da suka shude sun sha yin jawabai masu mahimmanci ga kasar da al'ummarta. Daren jiya shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya bayyana a kafofin labarai mallakar gwamnati domin yiwa al'ummar kasar jawabi. Jawabin ya zo daidai lokacin da kasar ke fuskantar rudani domin wasu dalilai masu nasaba da siyasa dangane da kokarin shugaban na kafa gwamnatin hadin gwuiwa da ta kunshi 'yan adawa.
Da ya juya kan gwamnatin hadi gwuiwa shugaban kasar ya ce yana alfahari da ita. Ya ce kafa irin wannan gwamnatin tamkar bude wata dama ce kan burin da yake da shi. Ya ce a ganinsa hanya ce ta kara karfafa dimokradiya. Bayan batun siyasa shugaban ya tabo wasu batutuwa masu mahimmanci kamar baiwa 'yan Niger dake kasashen waje damar yin zabe. Shugaban ya yabawa 'yan siyasa da yin baki daya domin wannan kudurin na baiwa 'yan Niger dake kasashen waje samun wakilci a majalisa.
Shugaban ya cigaba da cewa yana kokarin mika wata doka ga majalisar dokoki domin kara yawan mata a madafin iko. Dangane da hako ma'adanan kasa shugaban ya yi alkawarin bi sawu da kafa ya tabbatar an yi adalci da gaskiya yadda kasar zata anfana ainun. Akwai yarjejeniya ta bai daya da aka kulla da kamfanonin kasashen waje masu hakar ma'adanai a kasar. Kuma 'yan rajin kare hakkokin 'yan kasar na ganin cewa ya kamata a rika baiwa 'yan Niger damar cin gajiyar ma'adanan.
Abdullahi Mamman Ahmadu nada karin bayani.