Hukumar Kwallon Kafar Najeriya (NFF) ta tabbatar da nadin Eric Sekou Chelle a matsayin babban mai horas da tawagar kasar ta Super Eagles.
An cimma wannan matsaya ne a taronta da ya gudana a Abuja, a ranar Alhamis 2 ga watan Janairun da muke ciki, inda karamin kwamitin NFF kan kwarewa da ci gaba ya ba da shawarar nadin tsohon babban mai horas da tawagar kwallon kafar kasar Mali ta maza a matsayin sabon babban mai horas da tawagar Super Eagles.
"Kwamitin zartarwar NFF ya tabbatar da nadin a ranar talata 7 ga watan Janairun da muke ciki," kamar yadda NFF ta bayya a shafinta na yanar gizo.
Nadin nasa ya fara aiki nan take kuma hakkinsa ne ya jagoranci tawagar Super Eagles zuwa samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya na 2026 da hukumar kwallon kafar duniya (FIFA) ke shiryawa, inda za a fara wasannin zagayen gaba na shiga gasar (a ranar wasa ta 5 da ta 6) a watan Maris).
Dandalin Mu Tattauna