‘Yan sandan New Zealand sun ba da tabbacin cewa, mutum 31 yanzu haka suna asibiti kuma sun tabbatar da mutuwar mutane biyar.
“Ga wadanda suka mutu ko ‘yan uwansu suka bata da abokanansu, mun yi tarayya cikin bakin ciki wanda bazai musaltuba,” inji Firai Minista Jacinda Ardern ta bayyana a yau Talata.
“Wadanda kuke matukar kauna da suka tsaya a gaban Kiwis wadanda suka karbe ku anan, kuma muna jajanta muku.
Ardern ta fada cewa mutane 47 da suke tsibirin a lokacin da dutsen ya barke da aman wuta a ciki har da ‘yan New Zealand da dama, da kuma baki masu yawon bude ido daga Australia da Birtaniya, da Amurka da China da kuma Malaysia.
Rahotanin kamfanin dillancin labarai na AFP da kyamarori suka nuna abin da ya faru kai tsaye daga aman wutar da dutsen ya yi ya nuna wasu rukunin masu yawan bude idon suna tafiya a bakin dutsen kafin ya fara aman wuta.
Facebook Forum