Jami’ai sun ce wutar ta tashi ne da safe a ginin mai hawa 6 inda leburori su ke bacci, a tsohon garin birnin da ke kusa da yankin kasuwa mai cike da hada-hadar jama’a.
Masu ceto sun kai wadanda lamarin ya rutsa da su a asibiti. An yi wa wasu mutane 16 maganin kunar wuta ko kuma shakar hayaki suka kuma wartsake.
Jami’ai sun ce ana binciken musabbabin tashin gobarar da ta soma da misalin karfe 5:30 na safe.
Motocin kashe gobara 25 suka yi aikin kashe wutar, kuma tuni aka kammala aikin ceto, a cewar jami’in ‘yan kwana-kwana, Atul Kumar Gargs.
“Mun fitar da kusan mutane 52, an sanar da mu ne da karfe 5 da minti 22 na safe, kuma da farko mun tura motoci 4, ya zuwa yanzu motocin kashe gobara 35 muka tura, tare da adadin jami’ai 150.
An kai mutanen da aka ceto a asibitoci daban-daban. Ana iya samun adadin wadanda suka mutu da wadanda suka tsira a asibitocin. Kimanin mutane 2 kuma suna cikin karikicen har yanzu”.
Firai Minista Narenda Modi, ya bayyana gobarar a matsayin “babban ibtila’i”.
Tashin gobara ya kasance ruwan dare a Indiya, inda masu gini da mazauna ke take dokokin gine-gine.
Facebook Forum