Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya rattaba hannu kan wani kudurin doka na gyara wata doka ta yanzu wadda ke daukar wasu kafafen yada labarai a matsayin "'yan koren kasashen waje" da masu suka suka ce ana amfani da ita ne wajen murkushe duk wata adawa, da takaita labarai, da kuma dakile musayar ra'ayi.
Sabuwar dokar ta baiwa hukuma ikon sanya wa manema labarai dake aiki ga kungiyoyi da aka ayyana a matsayin “'yan koren kasashen waje” a matsayin wakilan kasashen wajen su kansu.
Za a yi amfani da wannan lakabin ga duk wanda ya ba da hadin kai ga da kafofin yada labarai na ƙasashen waje, kuma su ke samun tallafin kuɗi ko wasu tallafi na kaya daga gare su.
Facebook Forum