Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nelson Mandela Ya Rame Sosai


Mandela a Afirka ta Kudu
Mandela a Afirka ta Kudu

Tashar telebijin ta Afrika ta Kudu ta nuna wani sabon hoto na tsohon shugaban kasar Nelson Mandela, inda aka ga duk ya kara ramewa, ya raunana – wanda kuma ma wannan shine hoton farko da aka taba nunawa nashi tun bayan da aka sallamo shi daga assibiti a watan da ya gabata.

A cikin hoton, anga Mandela zaune, duk ya turnuke fuska, ba murmushi, yana kan wata kujera, an sa wani mayafi an rufe kafafunshi yayinda likitocinsa da wasu gaggan ‘yan siyasa, ciki harda shugaban kasar na yanzu Jacob Zuma, ke zagaye da shi, suna magana can a tsakaninsu.

Duk da cewa shi shugaba Zuma ya fito a kafar watsa labaran kasar ta SABC yana gayawa al’ummar kasa cewa Mr. Mandela yana samun sauki, wasu masu sharhi a duniyar gizo sunce su kam, a ganinsu, Mandela, 94, baya da alamar wanda ke morewa koshin lafiya, har ma suna zargin jagabannin jama’iyar ANC mai mulkin kasar da cewa suna anfani da shi wajen cimma biyan muradunsu ne kawai.

To amma ANC tace wannan hoton video da aka nuna, an nuna shi don anfanin jama’a, ba wai don cimma muradun siyasa na jam’iyyar ba. Jam’iyyar kuma ta ce ta tsaya daram akan bayanin da ta bada na cewa, duk da alamun raunin da ake gani ga Mandela din, yana dada samun sauki kuma yana cikin fara’a.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG