Ofishin shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya sanar da cewa, an salami Mandella dan shekara 94 yau asabar sabili da sauki da ya samu. Wannan ne karo na uku da aka kwantar da dan gwaggwarmayar yakin wariyar launin fatar a cikin watanni hudu.
Bayan an kwantar da shi a asibiti ranar 27 ga watan Maris, Afrika ta kudu ta bayyana cewa, ana yi mashi jinyar cutar huhu da kuma namoniya da yake fama da su.
Mr. Mandela wanda ya sami lambar yabo ta Nobel, yana fama da cutar namoniya tunda ya kamu da tarin fuka lokacin shekaru 27 da ya shafe a gidan yari sabili da yaki da yayi da wariyar launin fata, tsohon salon mulkin Afrika ta Kudu inda turawa ‘yan tsirarru suke mulki.
Ya zama shugaban Afrika ta Kudu bakar fata na farko a shekarar alib dubu da dari tara da casa’in da hudu, ana kuma daukarshi a kasashen duniya a matsayin gwarzo a fafatukar yaki da nuna wariya.