Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nelson Mandela Ya Koma Asibiti A Pretoria Domin Gwaji.


A wannan hot Nelson Mandela ne a bikincikarsa shekaru 94 da haifuwa cikin watan Yulin bara.
A wannan hot Nelson Mandela ne a bikincikarsa shekaru 94 da haifuwa cikin watan Yulin bara.
Fadar shugaban Afrika ta kudu tace gwarzon zaman lafiya wanda ya sami lambar yabo ta Nobel, kuma tsohon shugaban kasar, Nelson Mandela, yana asibiti domin a auna lafiyarsa.
Mac Maharaj, kakakin shugaban Afirka ta kudu, yace Mandela dan shekaru 94 da haifuwa yau Asabar ne yaje asibiti dake Pretoria babban birnin kasar, kuma babu wani abun tada hankali gameda lafiyarsa, a yayinda likitoci suke gwaji.

An kwantarda Mr. Mandela cikin watan Disemba domin cutar huhu.

Mr. Mandela yayi zaman kurkuku na kusan shekaru 30 saboda adawa da tafarkin mulkin nuna wariyar launin fata, ya zama tambari kuma jigon maida kasar kan tafarkin mulkin demokuradiyya, bayan shekaru na mulkin danniyar da tsiraru farar fatan kasar suka yi.

Ya zama bakar fata na farko da ya shugabanci Afirka ta kudu.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG