Mr. Zuma yau alhamis yayi wa dan shekaru tasa’in da hudu din, kuma mutumin da yaci lambar yabo ta nobel fatar samun lafiya, kuma ya nuna kwanciyar hankalinsa da likitocin da zasu duba Mr. Mandela.
Nelson Mandela dai ya shere sama da shekaru 30 a gida yari, saboda adawa da yayi da turawan mulkin mallaka da wariyar launin fata, kuma ya zama jigo wajen samar da mulkin demokradiyya ta hanyar lumana a wannan kasa. Shine ya zama bakar fata na farko da ya shugabanci Afirka ta Kudu.