Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Stephen keshi Zai Cigaba Da Baiwa Kananan ‘Yan Wasa Dama


Coach Stephen Keshi speaks to members of the Super Eagles at practice in Abuja before their World Cup qualifier against Ethiopia.
Coach Stephen Keshi speaks to members of the Super Eagles at practice in Abuja before their World Cup qualifier against Ethiopia.

Babban Koch ‘din Super Eagles Stephen Keshi, yayi alkawarin cigaba da baiwa kananan ‘yan wasan Najeriya damar kasancewa suna bugawa kungiyar wasa.

Stephen Keshi dai ya fara aikin sa na babban kochin Najeriya, bayan da ya rattaba hannu kan jarjejeniyar aikin shekaru biyu da hukumar kwallon kafar Najeriya (NFF).

An dai san shi wajen baiwa ‘yan wasan cikin gida damar nuna bajimtarsu, kuma ya nuna cewa bazai dai na yin hakan ba. inda yace, “a koda yaushe ina jin dadin aiki da kananan ‘yan wasa, wannan ba wani sabon abu bane a gareni, saboda ina yin hakan tun asali kuma zan cigaba da yi.”

Ya dai cigaba da cewa, kusa da tafiyar mu kasar Togo da Mali, ina baiwa kananan ‘yan wasa damar nuna kwazonsu kuma yawancinsu basu bani kunya ba.

Wannan wani abu ne da nake son cigaba dayi kuma ina son hakan ya taimaka min wajen gina kungiyar wasa mai kyau ga kasar mu.

A koda yaushe mukazo sansanin horon ‘yan wasa, na kalle su ina matukar farin ciki, kuma hakan nada kyau domin yawancin su sun zama ‘yan wasan da muke ji da su, kuma ina son cigaba da hakan.

XS
SM
MD
LG