Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zauren Matasa – Hujjojin Wasu Matasa Na Kara Aure


Daga Hagu zuwa Dama: Comrade Danjuma Bello Sarki, Shugaban Matasa na yakin neman zaben gwamna Yero da Bajoga a karkashin tutar jam’iyar PDP a Giwa, jahar Kaduna, da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na Kaduna ta tsakiya: da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na ja
Daga Hagu zuwa Dama: Comrade Danjuma Bello Sarki, Shugaban Matasa na yakin neman zaben gwamna Yero da Bajoga a karkashin tutar jam’iyar PDP a Giwa, jahar Kaduna, da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na Kaduna ta tsakiya: da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na ja

Cikin zauren matasa nayau da Mustapha Nasiru Batsari ya jagoranta a jihar Niger, matasa sun tattauna ne akan hujjojinsu na kara aure.

A tambayar farko da akayi wa Alhaji Murtala Mai Gyada, kan matsayinsa na matashi wacce irin hujja yake amfani da ita wajen yanke shawarar kara aure? Inda Alhaji Murtala, ya bayyana cewa babbar hujjar sa da yake amfani da ita wajen kara aure itace, yana ganin idan ya kara mata zata taimakawa gidansa wajen zamantakewa, musamman idan larura ta faru a gidan ko ta rashin lafiya, tafiya dadai sauransu hakan na iya taimakawa wajen tafiyar da harkokin gida ba tare da samun wata matsala ba.

Shikuma Mallam Atta, yayi nunin cewa yana amfani da tanadin dayake da shi wajen yanke shawarar kara auren, hakan na nufin dubawa da tabbatarwa cewa shin zai iya ‘daukar nauyin iyalinsa baki ‘daya har ma ya kara aure, idan yaga cewa zai iya to zai kara aure domin taimaka wajen rage cinkoson matan da ake dasu a cikin gari. Kasancewar yin hakan na rage wa iyaye lalurori da irin lalaci da ake samu a cikin al’umma, wannan shine dalilinsa na kara aure wanda a yanzu haka yana da mata biyu a gidansa yakuma ce idan ya kara samun wadata to zai kara ‘daya.

Sai kuma ra’ayin Mallam Isah, wanda yace shi yana amfani bisa ga maganar Allah ma ‘daukakin sarki, yace bayason yakasance cikin wadannan na karshe yana son kasance cikin matsakaita, wanda daga mata ‘daya zuwa biyu shine ra’ayinsa, wanda hakan na nunin cewa yana amfani da addini wajen yanke shawararsa ta kara aure.

Saurari cikakkiyar tattaunawar matasan.

XS
SM
MD
LG