Innalillahi wa’innailaihirrajiun, a jiya Lahadi bayan wata gadar tsallake babban titi a birnin Kano ta fado ta kashe kimanin mutane uku. Wannan abun ya farune da yamma bayan kamfanin da ke wannan aiki ya kamala aikinshi a jiyan, ita dai wannan gada ta fado inda tayi daidai da wata motar Tasi na wuce wa, sai ta fado a kan wannan mota kuma an samu rashi rai na mutane uku a nan take.
Da safiyar yau kuma Litinin sai daya bangaren wannan gadar ya sake fadowa inda kuma akayi dai dai da wasu bayin Allah a cikin a daidaita sahu ko kuma keke Napep, sun kawo wurin, amma Allah cikin ikon sa yasa wadanan bayin Allah basu rasa rayukansu ba sun dai samu raunuka.
Wannan wani abu ne da ya kamata hukumomi su dauki mataki da yakamata wajen hukunta wannan kanfani da kuma biyan diyya. Baya ga haka mutane su zamo masu lura da duk wasu ayyuka da ake gudanarwa a kan tituna don duba abunda ya dace kamin su aiwatar da wani abu.