Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Kwashe ‘Yan Kasar Daga Lebanon


Yusuf Tuggar
Yusuf Tuggar

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Amb. Eche Abu-Obe, ya ce dama kasar ta kwashe ‘yan Najeriya da ke kudancin Lebanon zuwa babban birnin kasar Beirut.

Gwamnatin Najeriya ta ce saboda tabarbarewar tsaro a gabas ta tsakiya, musamman fadan da ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas zata kwashe ‘yan kasar da ke Lebanon.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Amb. Eche Abu-Obe, ya ce dama kasar ta kwashe ‘yan Najeriya da ke kudancin Lebanon zuwa babban birnin kasar Beirut.

Tun a watan Agusta ofishin jakadancin Najeriya a Lebanon ke fitar da takardar gargadi da ba da shawara ga ‘yan kasar kan batun yadda zasu bar Lebanon ta hanyar jiragen fasinja da suke zuwa kasar.”

Sanarwar ta kara da cewa “ya zuwa yau dai babu wani dan Najeriya daya rasa ransa tun bayan barkewar fadan.”

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta tabbatar da cewa gwamnatin kasar na aiki da masu ruwa da tsaki don ganin an kare rayuwar ‘yan kasar a Lebanon har zuwa lokacin da za’a kwaso su zuwa gida Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG