Gwamnatin Najeriya ta yi nasarar mayar da 'yan kasarta 390 da suka makale a birnin Yamai, Jamhuriyar Nijar zuwa gida.
Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira, 'Yan Ci Rani da Masu Gudun Hijira a Cikin Gida (NCFRMI) ce ta karbe su a Makarantar Horas da Ma’aikatan Shige da Fice da ke Kano a cewar Voice of Nigeria (VON.)
Kwamishinan Hukumar NCFRMI na Tarayya, Tijjani Ahmed, wanda Mai Kula da Ofishin Kano, Hajiya Lubah Liman, ta wakilta, ya sake jaddada kudurin gwamnati na kare 'yan kasa da kuma sake hada su cikin al’umma.
Ya sanar da cewa wadanda aka dawo da su za su ci gajiyar shirye-shiryen tallafawa karkashin shirin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ke karawa jama’a kwarin gwiwa.
“Da isowar su, an yi wa dukkan wadanda aka dawo da su rijista tare da daukan bayanansu don samun damar shigar da su cikin shirye-shirye na ba da tallafin.” in ji Ahmed.
Dandalin Mu Tattauna