Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya ta amince da tsawaita lokacin yin rajistar zabe


Prof. Attahiru Jega
Prof. Attahiru Jega

Majalisar dattaban Najeriya ta amince da kara lokacin yin rajistar zaben da za a yi a kasar a cikin watan afrilu.

Majalisar dattaban Najeriya ta amince da kara lokacin yin rajistar zaben da za a yi a kasar a cikin watan afrilu, bayan da shugaban hukumar zaben kasar, Prof. Attahiru Jega ya bukaci ‘yan majalisar dokokin da su tsawaita lokacin yin rajistar zaben da wa’adin ta zai cika a ranar 29 ga wannan wata na janairu.

Shirin dokar wanda ‘yan majalisar wakilai su ka fara amincewa da shi, zai zama doka idan shugaba Goodluck Jonathan ya rattaba hannu akai. Idan hakan ta faru kuwa dokar za ta bada damar kammala yin rajistar zaben karkari wata daya kafin zabe maimakon watanni biyu.

Jega ya ce karin lokacin zai baiwa jami’ai damar yin rajista ga duka ‘yan Najeriyar da ake iya yiwa rajista, a lafazin shi.

Mutane miliyan saba’in ya kamata a yiwa rajista a kasar wadda ta fi yawan jama’a a nahiyar Afirka.

Jega ya nuna cewa ya na sane da matsalolin da aka samu daga fara yin rajistar zaben, amma ya ce ana shan kan su. Ya bayyana ranar da aka fara aikin rajistar da wani mawuyacin hali inda na’urori su ka yi ta kasa daukan hoton ‘yan yatsun mutanen da ake yiwa rajistar.

‘Yan Najeriya masu kada kuri’u za su zabi sabbin ‘yan majalisun dokoki da sabbin gwamnonin jahohi da kuma shugaban kasa.

Ana daukan zabubbukan da ke tafe tamkar mizanin auna nasarar Najeriya ta iya shirya zabe mai ingancin da kowa zai yarda da shi bayan tulin matsalolin da aka yi ta fama da su a zabubbukan da su ka wuce.

XS
SM
MD
LG