Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikici ya barke a Jos babban birnin Jihar Plateau


'Yan sandan kwantar da tarzoma na Najeriya
'Yan sandan kwantar da tarzoma na Najeriya

Wani sabon rikici da ya barke a Jos babban birnin jihar Plateau ya yi sanadin asarar rayuka da kaddarori.

Rahotanni daga jihar Plateau na nuni da cewa, wani sabon rikici ya barke a Jos babban birnin jihar, sakamakon zanga zangar da daliban jami’ar Jos suka yi na nuna rashin amincewarsu da harbin kan mai uwa da wabi da jami’an sojoji suka rika yi jiya da yamma. Wanda ya yi sanadin kashe wadansu dalibai uku da kuma raunata wasu da dama.An yi kone kone a unguwannin dake kewayen jami'ar Jos, yayinda mutane dauke da bindigogi suka rika fito mu gama da jami'an tsaron da aka ba umarnin yin harbi kan mai uwa da wabi kan duk wadanda aka samu suna tada zaune tsaye da kone konen wuraren ibada da kaddarori.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG